1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koma baya ga kungiyar IS a Iraki da Siriya

Salissou Boukari
March 8, 2017

Dakarun da ke yakar 'yan jihadi na IS a birnin Mosul na Iraki, sun sanar da irin koma bayan da 'yan jihadin ke fuskanta a Iraki da Siriya, inda ake ci gaba da fatattakar su.

https://p.dw.com/p/2Yo1b
Irak Kämpfe gegen IS in Mossul
Sojojin Iraki a birnin MossulHoto: Reuters/G. Tomasevic

Rahotanni daga birnin Mosul din dai na nuni da cewa, karfin kungiyar ta IS na ci gaba da raguwa a babbar cibiyarta da ke birnin, inda dakarun gwamnati suka kwace wasu sababbin unguwanni uku, sannan kuma karfinta na kara raguwa a yankin Aleppo na kasar Siriya, da ma birnin Raqqa inda 'yan kungiyar ta IS suka fi yawa a Siriyan. A ranar Talatar da ta gabata ne dai ke zaman rana ta uku da sabon samamen da sojojin na Iraki suka kaddamar a yammacin birnin na Mosul, wanda kuma suka samu ci gaba sosai a kokarinsu na kwato birnin baki dayansa daga hannun 'yan kungiyar IS din.

A halin yanzu dai sojojin sun kori 'yan jihadi daga yankin da ofishin gwamnan birnin na Mosul ya ke da cibiyar 'yan sandan jihar da kuma babban bankin kasar, inda a nan ne 'yan jihadi suka samu miliyoyin daloli lokacin da suka shiga birnin a shekara ta 2014.