Koma bayan iIimi a Afganistan
December 6, 2023A cewar kungiyar kare hakkin jama'a ta Human Rights Watch, matasa da dama za su rasa damar yin karatu a bisa sabon tsarin karatun da jadawalin karatun da gwamnatin Afganistan ta fitar. Babbar matsalar dai ita ce hana mata malamai shiga azuzuwa, wannan babbar barazana ce ga fannin ilimin boko, domin a baya ana da malaman makaranta mata da yawa, yanzu kuma kafin a samu maza da za su maye gurbinsu zai kasance babbar matsala. Wata babbar matsalar ita ce akasarin matasa suna tafiyar neman kudi domin ciyar da iyayansu, maimakon zuwa makaranta, wannan kuwa ya yi matukar karuwa tsakanin iyalai domin idan aka yi la'akari da yadda kasar ke fiskantar rushewar tattalin arziki, wanda ke tilastawa iyalai tafiyar neman abun sawa a baka a madadin tura 'ya'yansu izuwa azuzuwa don neman ilimi.