Mayar da Burkina Faso tsarin dimukaradiyya
February 23, 2022Gwamnatin mulkin sojan Burkina Faso tana duba shirin mayar da kasar bisa tafarkin dimukaradiyya cikin watanni 30, shekaru biyu da watanni 6 ke nan, kamar yadda wata majiya daga fadar shugaban kasar ta tabbatar a wannan Laraba. A watan Janairu sojoji suka yi juyin mulki a kasar da ke yankin yammacin Afirka.
Lt Kanar Paul-Henri Damiba ke zama sabon shugaban gwamnatin mulkin sojan wanda ya kwace madafun iko daga hannun tsohon Shugaba Roch Marc Kabore sakamakon matsalolin tsaro da suka mamaye kasar, kuma makonni biyu da suka gabata aka kafa hukumar tsara mayar da kasar bisa tafarkin dimukaradiyya.
Sojoji za su yi amfani da shekaru biyu da rabin da za su rike madafun ikon kasar wajen tabbatar da magance kalubalen tsaron da kasar ta Burkina Faso ta samu kanta. Kana hukumar ta ba da shawarar nada ministoci 20 da 'yan majalisar dokokin gwamnatin wucin gadi 51, kamar yadda wata majiya ta kusa da rahoton da aka gabatar wa sojojin ta tsaigunta.