1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Komawar Nawaz Sharif zuwa Pakistan

September 10, 2007

A yau da sanyin safiya tsofon piraministan Pakistan ya koma gida bayan zaman hijira na tsawon shekaru bakwai

https://p.dw.com/p/Btub
Magoya bayan Nawaz Sharif
Magoya bayan Nawaz SharifHoto: AP

Sai da aka sha fama da kai ruwa rana tsakanin tsofon P/M na Pakistan Nawaz Sharif da wasu askarawan kundumbala da suka kutsa cikin jirgin saman dake dauke da shi jim kadan bayan saukarsa suka kuma yi masa kawanya. Rahotanni na manema labarai dake wa Nawaz Sharif rakiya sun ce tsofon P/M ya ki ya mika wa mahukuntan shige da fice na Pakistan takardarsa ta paspo. Tun kafin tashinsa daga birnin London a jiya lahadi Nawaz Sharif yayi tsokaci da cewar mai yiwuwa gwamnatin shugaba Musharraf tayi yunkurin tsare shi ko kuma ta fatattake shi daga kasar. Nawaz Sharif ya ce amma baya fargaba ko tsoron barazanar da Musharraf ke masa game da sake tasa keyarsa zuwa kurkuku:

“Ya ce zai tsare ni kai tsaye a gidan kurkuku. Ba na tsro, bana fargabar haka. Ya tsare ni tsawon watanni 14 bayan kifar da gwamnati ta ta yayi, amma tun daga wannan rana na shiga gwagwarmaya. Ina gwagwarmaya ne domin sake dawowa da mulkin demokradiyya.”

An dai saurara daga kakakin ministan cikin gida birgediya Javal Iqbal Cheema yana mai fadin cewar za a yi ma’amalla da Nawaz Sharif ne daidai da abin da doka ta tanada bayan saukarsa. Kafin saukar tasa dai mahukuntan Pakistan sun tsare mutane dubu hudu daga cikin magoya bayansa da kuma wasu daga cikin shuagabannin jam’iyyarsa ta kungiyar hadin kan Pakistan, abin da ya hada har da shugaban jam’iyyar. Kazalika da wasu shuagabanni uku na wata kungiyar hadin guiwar addini. A shekara ta 1999 ne Musharraf ya kifar da gwamnatin P/M Nawaz Sharif ya kuma tilasta masa zaman hijira har tsawon shekaru 10 a karkashin wata yarjejeniyar da suka cimma. Komawar tasa a yanzu ka iya zama mummunar kalubala ga shugaba Musharraf, wanda gwamnatinsa ke zargin tsofon P/M da rashin cika alkawari a daidai wannan lokacin da kasar Pakistan ke bukatar kwanciyar hankali a zaben majalisar dokoki da majalisun gundumomin da za a gudanar tsakanin 15 ga satumba zuwa sha 15 ga oktoba mai zuwa. Nawaz Sharif yayi watsi da kiran da Saudiyya tayi masa da ya ci gaba da zaman hijirar kamar yadda aka shirya domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin Pakistan.