1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Arewa: Inganta noman shinkafa a Afirka

Binta Aliyu Zurmi
July 6, 2023

Koriya ta Kudu na shirin rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniya da kasashen Afirka 8 domin taimaka musu inganta harkokin noman shinkafa da ma kaucewa dogaro da shigar da kayayakin abinci daga ketare.

https://p.dw.com/p/4TXRW
Südkoreas Präsident Yoon Suk-yeol
Hoto: Daewoung Kim/REUTERS

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ne ya labarta hakan bisa wata sanarwar ta ministan noma na kasar, wanda ke zuwa a daidai lokacin da nahiyar ke fuskantar barazana ta karancin abinci.

Karkashin wannan shiri, Koriya ta kudu za ta samar da manyan gonakai a kasashen Ghana da Gini da Gini Bissau da Gambiya da Senegal da Kamaru da Yuganda gami da kuma Kenya domin samar da wani sabon nau'i na shinkafa.

Sama da dalar Amurka miliyan 77 ne wannan shirin samar da shinkafa a kasashen na Afirka zai lakume nan da shekaru 4 da ke tafe.