1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Arewa ta sake yin gwajin makamai

Mouhamadou Awal Balarabe
July 22, 2023

Amurka da Koriya ta Kudu da ke dasawa da juna sun bayyana cewar suna nazarin gwajin Koriya ta Arewa tare da sa ido kan alamomin karuwar harba makamai masu linzami.

https://p.dw.com/p/4UFlD
Nordkorea Unbekannter Ort | Teststart einer Hwasong-18 Interkontinentalrakete
Hoto: KCNA via REUTERS

Koriya ta Arewa ta harba makamai masu linzami da dama a yammacin rawayar teku, a cewar hafsan hafsoshin sojojin Koriya ta Kudu. Sai dai Amurka da Koriya ta Kudu da ke dasawa da juna sun bayyana cewar suna nazarin gwajin tare da sa ido kan alamomin karuwar harba makamai na fadar mulki ta Pyongyang.

Dama dai dngantaka tsakanin Koriya ta Arewa da takwarta Koriya ta Kudu ta yi tsami a baya-bayannan. Ko da a kwanakin da suka gabata, sai da shugabannin mulkin gurguzu na Koriya ta Arewa suka yi ta gwajin makamai masu linzami akai-akai. Amma a martanin da ta mayar, Amurka ta sanar da tura wani jirgin ruwa mai dauke da makaman nukiliya a kasar Koriya ta Kudu domin bata kariyar da take bukata.