1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaKoriya ta Arewa

Pyanyong za ta sake gwajin nukiliya

Abdul-raheem Hassan MNA
October 17, 2023

Koriya ta Arewa ta jaddada cewa shirinta na mallakar makaman nukiliya wani mataki ne na kare kanta daga barazana, tare da daura aniyar tinkarar barazanar yakin nukiliya daga Amirka.

https://p.dw.com/p/4Xc6I
Shugaban Korea ta Arewa, Kim Jong UnHoto: KCNA/REUTERS

Kim Kwang Myong wanda kafar yada labaran kasar KCNA ta bayyana a matsayin mai bincike a cibiyar kwance damarar makamai da zaman lafiya ta ma'aikatar harkokin waje, ya zargi Washington da haddasa husuma a yankin da shirinta na nukiliya, tare da dora mata alhakin rashin zaman lafiya da ke lalata zaman lafiya a duniya.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Pyanyong ta yi gargadi a yankin ta hanyar harba makamai masu linzami akai-akai da iya cimma Amirka.