1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaKoriya ta Arewa

Koriya ta Arewa ta harba makamai masu linzami daga teku

August 21, 2023

Koriya ta Arewa ta ce harba makamai masu linzamin da Shugaba Kim Jong un ya umurta a tekun Japan na nuna cewa babban jirgin ruwan yaki na kasar na aiki kuma zai iya kai hari idan bukatar hakan ta taso.

https://p.dw.com/p/4VOKB
Hoto: KCNA/KNS/dpa/picture alliance

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya halarci wani atisayen sojin ruwa na musamman wanda ya umurci a gabansa jirgin ruwan yaki na kasar ya harba makamai masu lunzami a matsayin gwaji. Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Amirka da makwabciyar kasar, Koriya ta Kudu, suka shirya gudanar da wani atisayen sojoji na musamman wanda kan haifar da karuwar tashin hankali a tsakanin Koriyoyin guda biyu a duk lokacin da aka yi shi.

Duk da Koriya ta Arewan ba ta bayyana zahirin ranar da shugaban nata ya ziyarci sojojin ruwan domin cilla makamai masu linzamin ba, amma Koriya ta Kudu ta ce labarin cike yake da kura-kurai.