Kosovo ta zama ƙasa mai cikkaken 'yanci
September 10, 2012Bayan shekaru huɗu da rabi da ɓallewa daga Sabiya, ƙasar Kosovo ta yi bikin samun cikkaken 'yanci.
A yammacin wannan Litinin a birnin Pristina, babban birnin ƙasar, Komitin ƙasashe 25 da ya jagorancin ɓallewar Kosovo ya aje aiki, domin miƙawa hukumomin ƙasar ragamar al'amura gaba ɗaya.To saidai wannan komiti tare da haɗin gwiwar tawagar ƙungiyar tarayya Turai, zai ci gaba da sa ido har sai lokacin da ƙasar ta zauna da gindinta.
Daga bayana 'yancin kan ƙasar Kosovo a shekara 2008 zuwa yanzu ƙasashe 90 na duniya suka amince da ita.To saidai Sabiya na adawa hakan, amma ƙungiyar tarayya Turai ta gittawa hukumomin Sabiya sharaɗin ƙulla kyakkyawar ma'amala da Kosovo, kamin Sabiya ta samu karɓuwa a matsayin memba a sahun ƙasashen EU.
Mawallafi:Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe