1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotin ƙolin Spain ta yanke hukunci ag ame da harin shekara ta 2004

Yahouza S.MadobiOctober 31, 2007

Sakamakon hukunci ɗaurin shekaru dubu 40 ga yan ta´adan da su ka kai harin Madrid a shekara ta 2004

https://p.dw.com/p/C14n

Yau ne kotun ƙasar Spain, ta yanke hukunci, ga mutanen da a ke zargi da hannu a cikin hare-haren ta´adanci da su ka wakana a birnin Madrid, ranar 11 ga watan Maris shekara ta 2004.

Shugaban kotun kolin ƙasar Spain kenan Javier Gomez Bermudez ke karanta tukume-tuhumen da su koti ke wa munaten da aka asamu da hanu acikinhare. Harenta adanci Spain na shekara ta 2004, wanda sun hadasa mutuwar mutane 191 daidai, sannan kusan dubu 2 su ka ji raunuka.

Baki ɗaya bama-bamai 10 su ka tarwawatse a cikin jiragen kasa 4, dake kai da kawo tsakanin birnin Madrid da yankunan da ke keywayer da birnin.

Wannan shine hari mafi muni ,da kungiyar Alqai´da ta kai,tun bayan wanda ya wakana a ƙasar Amurika ranar 11 ga watan satumber shekara ta 2001.

Mutane 28 , kotun ta tabbatar da cewar, su na da hannu dumu dumu, a cikin wannan mummunan hari.

Hukunce-hunkuce da aka kotu ta yanke, da sauran bayanan da ta gabatar, na ƙunshe a cikin wani babban littafi mai shafi a ƙalla 600.

A cewar Pilon Manjon, da ya halarci kotun shari´a akwai alamun yanke hukunci mai tsananai a mutanen 28.

„Ta la´akari da binciken da ƙurraru su ka gudanar, wanda kuma ya bada shaidi lefin da ake tuhumar su da aikatawa, a gani na za su fuskanci hukunci mai tsanani“.

Babban jujun da ya shigar ƙaran Javier Zaragoza, ya buƙaci kotu ta yanke hukunci ɗaurin shekaru dubu 40, a kurkuku, ga 8 daga cikin mutanen da aka gurfanar da da su.

Wannan mutane 8 sun haɗa da 2 wanda su ka aza bama-baman da su ka tarwatse da kuma 3 wanda su ka kitsa wannan hari.

Wanda su ka shirya harin sune, Rabei Usmane Sayid Ahmed da aka fi sani da suna Mohamed ɗan Masar, sai kuma yan kasar Marroko 2, wato Yussef Belhaji da Hassane Al Haski.

Mai shari´a Zaragoza ya ci gabada cewa.

„ Akwai shaidu cikkaku, babu shati faɗi a game da binciken da aka gudanar , a game da haka kotu zata yanke hukunci da ya dace.“

Cemma kamin hukunci na yau ,wata kotu ta birnin Madrid, ta yanke wa mutanen 8, hukunci ɗaukin shekaru kussan dubu ɗari 3 da 12 a kurkuku a zaman sharia´a da ya wakana daga watan feburyaru, zuwa juli na wannan shekara.

Dukan wanda aka tuhuma da lefikan kai harin,sun musanta wannan zargi.

To saidai a lokacin da ta bada hukunci ƙarshe kotun ƙolin ƙasar Spain ta tabbatar da ɗaurin shekarun dubu 40, kamar yadda alkali mai shigar da ƙara ya buƙata ga 3 daga cikin manyan masu lefin, wato Jamal Zougoum dankasar Marroko, Otman El Gnaoui da kuma Jose Emilio Suarez dankasar Spain.

A daya wajenkotu ta yanke hukunci ɗaurin shekara 20 ga Yussef Belhaj ,da kuma Hassane Al Haski saboda haɗin kann da su ka bada.

Saidai a wani mataki da ba a zata ba, ta yi belin Mohamed ɗan Masar mutumen da ake dauzkar tamakar wanda ya jagoranci harin daga duk wata tuhuma,haka zalika, ta ce babu hannun ƙungiyar yan ware ta ETA a cikin wannan hari.

A jimilce kotun ta yi belin 7 daga mutane 28 da ake tuhuma da hannu acikin wannan hare haren ta´danci.