1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masar ta rataye mutanen da suka kashe 'yan sanda

Abdul-raheem Hassan MNA
April 26, 2021

Hukuncin ya biyo bayan kamen da aka yi bayan zanga-zangar adawa da matakin sojin Masar na hambarar da tsohon Shugaban kasar Mohammed Morsi shekaru kusan goma da suka gabata.

https://p.dw.com/p/3sbaV
Ägypten Anti-Mubarak Demonstration Prozessbeginn
Hoto: dapd

Wata kotu a kasar Masar ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya kan mutane tara da ake zargi 'yan kungiyar IS ne da suka kashe jamai'an tsaro 14 a ofishin 'yan sanda a shekarar 2013 a wajen birnin Alkahira.

Hukuncin kisan ya fuskancir zazzafar adawa daga kungiyoyin kare hakkin bil Adama, wadanda ke cewa Masar ta kashe mutane sama da 100 a shekarar 2020 kadai, adadin da ya ninka hukuncin da take yi har sau uku a cikin shekara daya.