SiyasaAfirka
Kotu a Najeriya ta yanke wa 'dan kasar Sin hukuncin kisa
March 26, 2024Talla
Kotun ta samu Frank Geng-Quangrong, da laifin kashe budurwarsa mai suna Ummukulsum Sani da ka fi sani da Ummita a watan Satumbar shekara ta 2022 a jihar Kano.
Karin bayani: Kotu ta yanke hukuncin kisa kan makashin Hanifa
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito cewa za a gaggauta yanke masa hukunci idan har ya gaza daukaka kara kan hukuncin da kotun da ke zamanta a jihar Kano ta yi.
Karin bayani: Kano: Hukuncin kisa ga Sheikh Abduljabbar
Babu wanda ya fi karfin doka kuma dole ne kowa ya yi amfani da dokoki da al'adu na al'ummar jihar Kano ba tare da la'akari daga inda ya fito ba, acewar kwamishin shari'a na jihar Kano Barista Haruna Isa Dederi.