1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu a Pakistan ta ɗage shara'ar fraministan ƙasar

January 19, 2012

Kotun na zargin Yuzuf Raza Gilani da laifin ƙin ba da izinin na gudanar da bincike akan zargin da ake yi wa shugaban ƙasar na laifin aikata cin hanci

https://p.dw.com/p/13lt6
©Philippe Sterc/Wostok Press/MAXPPP France, Paris 04/05/11/11 Yousouf Raza Gilani Premier ministre de la Republique Islamique du Pakistan est recu a l Elysee M. Yousouf Raza Gilani prime minister of islamic republique of Pakistan is received at the Elysee Palace
Yusuf Raza Gilani fraministan PakistanHoto: picture alliance/dpa

Kotun ƙolin ƙasar Pakistan ta ɗage sauraron shara'a framinista Yusuf Raza Gilani har yazuwa ɗaya ga watan feberu,hakan kuwa ya biyo bayan da framinista ya baiyana a gaban kotu domin ba da bayani akan dalilian ƙin bada izini ga ƙasar Switzerland domin gudanbar akan tuhumar da ake yi wa shugaba Asif Ali Zardari da laifin cin hanci .Wani mashawarcin shugaban ƙassar ya shaida cewar jama'a na kallon wanna badaƙala a matsayin wani karon bata ƙarfe ne tsakanin sojojin da majalisar dokokin ƙasar.

Mista Gilani dai ya ce shugaban ya na da kariya ga duk wata tuhuma, to sai dai kuma masu ailko da rahotannin sun ce idan har kotun ta samu framistan da laifin takurawa alƙalanto kam wannan ya na iya zama sanadiyar rasa matsayin sa.Tun a shekara ta 2009 kotun ta buƙaci gwamnati ta rubata wasiƙa ga kasar Switzerland domin ba da dama su gudanar da bincikke akan zargin amma kuma ta yi watsi da buƙatar.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu