SiyasaTurai
Kotu ta aike da Shugaba Sarkozy gidan kaso
September 30, 2021Talla
Dokokin Faransa sun amincewa 'yan takarar shugabancin kasar su kashe kudin da ba su wuce Euro miliyan 22.5 ba, amma sai aka wayi gari Sarkozy ya kashe Euro miliyan 43 a yakin neman zaben nasa. Kotun ta ce Sarkozy ya san da wannan dokar amma, ya take sani, ya saba ka'ida.
A sakamakon wannan laifi, kotun ta tura tsohon shugaban kasar gidan kaso na shekara daya. Sai dai kuma tsohon shugaban na Faransa ya ce zai daukaka kara.