1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaruma za ta shiga gidan yari a Yemen

Abdul-raheem Hassan
November 8, 2021

Wata kotun 'yan tawayen Houthi a Yemen da gwamnatin Iran ke marawa baya, ta yankewa jaruma Intisar al-Hammadi hukuncin shekaru biyar a gidan yari bisa zargin ta da rashin da'a da shan kwayoyin sa maye.

https://p.dw.com/p/42jU8
Jemen Entisar al-Hammadi
Hoto: FACEBOOK/AFP

Hukuncin kotun ya shafi wasu mata uku abokan tafiyar jarumar, inda aka yanke musu hukuncin dauri a gidan yari. An kama jarumar Intisar al-Hammadi mai shekaru 20 da abokan sana'arta a watan Fabrairun 2021 yayin da suke zuwa daukar sabon bidiyo a babban birnin kasar Sanaa.

Tun bayan da mayakan Houthi suka kwace iko da Sanaa babban birnin kasar Yemen a 2014, suka fara gangamin tilasta mata bin da'a, matakin da hukumomin kare hakkin dan dam ke tir da shi. Lauyoyin da ke kare jaruma Intisar al-Hammadi sun ce tasirin jarumar a shafukan sada zumunta ne dalilin kamata.