Sarkozy zai yi zaman yari
March 1, 2021Talla
Wata kotu a Faransa ta yanke wa tsohon Shugaban kasar Nicolas Sarkozy hukuncin zaman yari tsawon shekaru uku kan laifin cin hanci da sayer da kayayyakin gwammnati ba bisa ka'ida ba.
Shari'ar na zama irinta na farko da wata kotu ta yanke wa tsohon shugaban kasa a Faransa kan zargin cin hanci, sai dai akwai yiwuwar Sarkozy zai daukaka kara kan wannan hukunci, duk da cewa hukuncin ya ba shi damar neman sassaucin daurin gida.