1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Paris: Ana shari'ar mutane 20 kan harin 2015

Abdul-raheem Hassan
September 8, 2021

An tsaurara tsaro a yankuna da dama na kasar Faransa, inda ake shari'ar mutane 20 da ake zargi da kitsa harin ta'addanci a birnin Paris ranar 13 ga watan Nuwamban 2015, wanda ya kashe mutane 130 tare da jikkata wasu 350.

https://p.dw.com/p/404mU
Frankreich | Prozessauftakt zum Pariser Terroranschlag vom November 2015
Hoto: Thomas Coex/AFP/Getty Images

Daga cikin mutanen da ke fuskantar shari'ar akwai Salah Abdeslam, wanda tuni aka same shi da laifi a kasar Belgium dangane da harbe-harben da aka yi lokacin, hukumomi sun kama shi a birnin Brussels a shekarar 2016.

Harin da aka kai shi a wani farfajiyar kade-kade a wajen wani filin wasan kwallon kafa a Faransar, ya ya girgiza duniya, kuma kungiyar IS ta dauki alhakin kai harin na wancan lokacin.