Kotu ta jingine zaman majalisar Kataloniya
October 5, 2017Kotun tsarin mulki ta kasar Spain a ranar Alhamis din nan ta zartar da hukuncin jingine zaman musamman da majalisar dokokin Kataloniya ta kira domin tattauna ballewa daga Spain.
Jam'iyyar gurguzu ta Kataloniya PSC mai ra'ayin kasancewar yankin a cikin Spain wadda kuma har ila yau ta ke adawa da yunkurin ballewar yankin, ta shigar da karar gaban kotu tare da hujjojin cewa ayyana 'yancin kan ya sabawa kundin tsarin mulki sannan zai rusa matsayin 'yan majalisun dokokin yankin na Kataloniya.
Dakatarwar da kotun tsarin mulkin ta yi, ya zo kwana daya bayan gwamnatin hadaka ta yankin ta yi kiran ayyana ballewa a ranar Litinin mai zuwa wanda zai shata sabuwar makoma ga yankin yayin da al'ummar suka kada kuri'ar ballewa daga Spain a kuri'ar raba gardamar da suka gudanar a ranar Lahadin da ta gabata.