1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta shirya yanke hukunci kan nasarar Tinubu

September 4, 2023

Watanni bayan kafuwar gwamnati a Najeriya, kotu ta ce ta kammala shirye-shiryen bayyana hakikanin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da 'yan hamayya ke kalubalanta.

https://p.dw.com/p/4VwMN
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola TinubuHoto: Gbemiga Olamikan/AP/dpa/picture alliance

Kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa a Najeriya, ta bayyana Larabar da ke tafe shida ga wannan watan a matsayin ranar da za ta yanke hukunci kan wanda ya lashe zaben watan Fabrairu.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ke mulki a yanzu dai na fuskantar gagarumin kalubale daga abokan karawarsa a zaben da suka hada da dan takarar PDP Atiku Abubakar da ya zo na biyu da kuma Peter Obi na Jam'iyyar Labour wanda ya zo na uku.

Wani babban aiki da ke gaban Shugaba Tinubun ma dai, shi ne matsin tattalin arziki da 'yan Najeriyar ke ciki da ma rashin tsaro da duk ke bukatar aiki tukuru.

Magatakardan kotun wanda ya sanar da Larabar a matsayin ranar yanke hukuncin, ya ce za a watsa zaman kotun kai tsaye ta kafafen labarai ciki har da talabijin.

A karshen watan Mayun da ya gabata ne dai aka rantsar da Bola Tinubu a matsayin shugaban Najeriyar, duk da kalubalen nasarar tasa.