An soke karin kudin ga 'yam majalisar Jamhuriyar Nijar
December 21, 2022Kotun ta yi watsi da karin kudin ‚yan majalisar a bisa hujjar cewa kudin 'yan majalisar sun wuce mizani idan aka kwatanta da yanayin talauci da akasarin 'yan kasar suke fama da shi. Tuni kuma kungiyoyin kare hakkin dan Adam da sauran 'yan kasa suka soma tofa albarkacin bakinsu kan matakin kotun.
A cikin wata takardar hukunci da ta fitar, kotun tsarin mulkin kasar ta Jamhuiriyar Nijar ta ce ta yi watsi da dokar alawus din 'yan majalisar dokokin domin sun kara wa kansu alawus na kudi miliyan tara-tara na CFA a kowace shekara, lokacin da kudin da kowane dan Nijar ke samu a shekara ya ja baya da kusan kaso biyu da rabi cikin dari a shekara ta 2021. Kazalika kotun tsarin mulkin ta ce ‘yan majalisar sun kara wa kansu kudin alawus din ba tare da sun bayar da shawarar hanyoyin da Nijar za ta bi ta samu karin kudin shiga ba ko da gwargwadan wadanda suka kara wa kansu ne. Da yake tsokaci kan hukuncin kotun Honnorable Kalla Moutari ya ce majalisar za ta yi nazarin hukunci a nan gaba ta san yadda za ta bullarwa lamarin.
Tuni dai wasu 'yan kasa suka soma tofa albarkacin bakinsu a kai hukuncin Kotun. To sai dai daga nata bangare kungiyar Muryar Talaka mai fafutikar kare hakkin dan adam da demokradiyya a Nijar ta bakin shugabanta Malam Nassirou Seidou cewa ta yi hukuncin da kotun tsarin mulkin ta yanke na kara tabbatar da 'yancin da fannin shari'a yake da a kasar.
A ranar 23 ga watan Nowamban jiya ne dai illahirin ‘yan majalisar dokokin kasar ta Jamhuriyar Nijar na bangaren adawa da na masu mulki su 151 da suka halarci zaman a wannan rana, suka kada kuri'ar amincewa da wannan doka ta kudin alawus din nasu, dokar da suka ce ba ta tanadi karin ko dala daya ba daga yadda ‘yan majalisar suka saba samu, hasali ma sun yi asarar kusan jika sha bakwai-bakwai. Batun da a yau kotun tsarin mulkin ta ce ba gaskiya ba ne. Yanzu dai ‘yan kasa sun zura ido su ga yadda ‘yan majalisar dokokin za su bular wa wannan hukunci na kotun tsarin mulkin.