Kotu ta tabbatar da hukunci ga Karim Wade
August 20, 2015A watan Maris ne dai da ya gabata wata kotu ta yanke wa Karim Wade wannan hukunci tare da tarar kudi Euro milian 210, amma kuma lawyoyinsa suka daukaka kara a gaban kotun kolin kasar wadda ita kuma ta kara jaddada wannan hukunci ba tare da halartar Karim Wade din ko kuma lawyoyinsa ba. Kotun dai ta yi watsi da hujjojin da Karim Wade ya gabatar a gabanta na neman ta karya hukuncin da aka yi masa na ran 23 ga watan Maris, inda ya zargi alkallan da bangaranci, abun da kotun kolin kasar ta Senegal ta ce wannan zargi bashi da tushe balle makama. An dai zargi Karim Wade da laifin mallakar wasu tarin kudade da yawansu ya kai Euro milian 178 ba bisa hanyar gaskiya ba a lokacin da ya ke minista kuma mai bada shawara ga mahaifinsa Abdoulaye Wade a lokacin da ya ke shugaban kasa.