Dangin Bazoum za su shaki iskar 'yanci daga hannun soja
April 3, 2024A cikin watan Oktoban 2023 hukumar mulkin soja ta CNSP ta sanar da dakile wani shiri da ta ce wasu sun kitsa na neman ficewa da hambararren shugaban kasa Mohamed Bazoum daga inda ake tsare da shi domin tserewa zuwa makobciyar kasa Najeriya ta hanyar wani jirgi mai saukar angulu.
Karin bayani : Lauyoyin Bazoum sun bukaci ECOWAS ta nemi sakinsa
Bayan wannan sanarwar jami'an tsaro suka kai samame a wani gida da ke unguwar Tchangarai a Niamey inda suka kama gwamman mutane akasarinsu na kusa da hambararren shugaban kasar da suka hada da Abdourahamane Ben Hamaye da Mohamed Mbarek da ake bayyana a matsayin jagororin shirin inda ake tsare da su a ofishin jami'an jandarma na birnin Yamai watanni sama da shida.
Bayan kalubalantar matakin tsare su ne kotun ta birnin Niamey ta ba da umurnin sakin mutanen biyu wanda ta ce ana tsare da su ba a kan ka'ida ba.
Karin bayani : Kotu ta saki dan Bazoum Mohammed
Kotun a Niamey ta ce gwamnati Nijar na da dama daukaka kara a cikin kwanaki 15 daga ranar biyu ga wannan wata na Aprilu.
Sai dai kotu ta ce ko tana da niyyar daukaka kara ya zama dole a gare ta saki mutanen biyu ko kuma tarar biyan miliyan daya a kowane yini ga mutanen ya hau kanta.