1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burtaniya: Hukunci mai tsauri kan lafin kisan jarirai

August 21, 2023

Kotu a Burtaniya ta yanke wa likitar da aka samu da laifin kisan jarirai bakwai da aka haifa da larurar rashin kosawar wasu sassan jikinsu, hukuncin daurin rai da rai.

https://p.dw.com/p/4VQ6O
Lucy Letby, likita a Burtaniya
Kotu a Burtaniya ta yanke wa ma'aikaciyar jinya hukuncin daurin rai da raiHoto: Cheshire Constabulary/AP Photo/picture alliance

A wannan Litinin ce kotun birnin Manchester ta yanke wa ma'aikaciyar jinya Lucy Letby mai shekaru 33 da haihuwa hukuncin daurin rai da rai, bayan ansa laifin kisan jarirai bakoye da kuma yunkurin kisan wasu shida. 

Karin bayani: Ma'aikaciyar jinya ta kashe jarirai a Burtaniya

Kotun ta yanke wa likitar wannan hukunci mafi tsauri da ba a cika yanke wa masu laifi a kasar ba, a yayin zaman da ta yi a wannan Litinin wanda aka watsa kai tsaye a kafar talabijin din kasar.

Dama dai a ranar Jumma'a da ta gabata gwamnatin Birtaniya ta bayar da umurnin gudanar da bincike kan cikin irin yanayin da Lucy Letby ta aikata kisan, binciken da ake sa ran zai kwantar da hankulan samar iyayen jariran, domin rage masu radadin damuwar da wannan al'amari ya saka a ciki.

Lucy Letby dai ta aikata wadannan laifuka a tsakanin watan Yunin shekara ta 2015 zuwa Yunin shekara ta 2016 a wani asibiti da ake kira Countess of Chester da ke birnin Liverpool a Arewa maso Gabashin Burtaniya.