Kotu za ta yanke hukunci kan zaben Najeriya
September 6, 2023An kwashe kusan watannin bakwai, alkalai biyar na sauraran korafe-korafe daga jam'iyyar PDP mai adawa da ta zo na biyu a zaben da kuma ta Labour Party wacce ta zo na uku. Atiku Abuubakar na neman kotu ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben ko kuma ta soke shi gabaki daya bisa zargin tafka magudin zabe, yayin da Peter Obi shi ma ya bukaci a soke zaben don a gudanar da wani sabo.
Karin bayani: Najeriya: Korafe-korafe kan sakamakon zaben 2023
Za a watsa zaman kotun kai tsaye a gidajen talabijin din kasar da sauran kafofin watsa labarai. Jam'iyyar APC ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ce ba ta da wani fargaba a kan yadda hukuncin kotun zai kasance, kuma ta yi amannar cewar ita za ta samu nasara a shari'ar.
Ko ma ya hukuncin kotun ya kaya, jam'iyyun PDP da LP na da dama sake daukaka kara zuuwa kotun koli.