Kotun EU ta soke tallafin ceto ga Lufthansa
May 10, 2023Talla
Kotun ta ce tun farko bai kamata hukumar tarayyar Turan ta amince da hukuncin da gwamnatin Jamus ta yanke na bai wa kamfaninn na Lufthansa tallafin ba.
A lokacin annobar Corona kasashen tarayyar Turai sun rika yin sassauci ga tsauraran dokokin EU na ba da tallafin ceto ga kamfanoni wanda ya sa hukumar tarayyar Turan ta amince da tallafin euro biliyan shida ga kamfanin Lufthansa a watan Junin 2020 wanda gwamnatin Jamus ke da hannun jarin kashi 20 cikin dari a cikinsa.
Kamfanonin jiragen sama na Ryanair da Condor Air suka shigar da karar inda suka ce an yi musu rashin adalci wajen ba da tallafin.