Kotun Hague na shirin yanke hukunci akan Charles Taylor
April 25, 2012Gwamnatin kasar Liberia ta bukaci jama'a su kwantar da hankula su kuma zauna lafiya gabanin hukuncin da kotun musamman ta kasa da kasa za ta yanke a ranar Alhamis akan shari'ar tsohon shugaban Liberia Charles Taylor. Shugabar kasar ta Liberia Ellen Johnson Sirleaf a cikin wata sanarwa ta bukaci jama'a su cigaba da yiwa kasar addu'ar zaman lafiya da kwanciyar hankali. A ranar Alhamis din nan ne dai kotun ta Majalisar Dinkin Duniya dake Hague za ta baiyana hukunci akan shari'ar ta Charles Taylor wadda aka shafe shekaru shida ana gudanarwa. Ana dai tuhumar Charles Taylor ne da laifukan yaki goma sha daya wadanda aka aikata a lokacin yakin Saliyo a tsakanin shekarun 1991 zuwa shekara ta 2002.
Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Umaru Aliyu