1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun Hague ta hukunta Charles Taylor

Zainab MohammedApril 26, 2012

Kotun shari'ar manyan laifunka da ke Hague ta ƙasar Netherlands, ta samu tsohon shugaban Liberiya Charles Taylor da laifukan yaƙi na tallafa wa mayaƙan tawayen Saliyo da makamai akan musayar lu'u-lu'u.

https://p.dw.com/p/14lQU
** FILE ** Former Liberian President Charles Taylor makes his first appearance at the Special Court in Freetown, in this April 3, 2006 file photo. Taylor's lawyers need more time to prepare his defense against charges he directed a campaign of murder, rape and enslavement in West Africa, his lawyer told a judge Friday Jan. 26, 2007. (AP Photo/George Osodi, Pool, File)
Hoto: dapd

Hukuncin na Taylor dai na mai zama na farkon irinsa akan wani tsohon shugaban ƙasa na Afirka da aka gurfanar a gaban wannan kotun Duniya. Da yake gabatar da shari'ar, Alkali Richard Lussick ya sanar da cewar a ranar 30 ga watan Mayu ne za'a sanar da irin hukuncin da aka yanke masa. Mai shekaru 64 da haihuwa dai, CharlesTaylor na fuskantar laifuffukan tallafa wa 'yan tawayen Saliyo mai arzikin albarkatun kasa, a yaƙin basasan da ya kashe mutane dubu 120. A cewar Dr Jibril Musa na cibiyar nazarin democraɗiyya dake abujan Najeriya, wannan babban darasi ne ga dukkan shugabannin da ke kan karagar mulki a Afrika. Acewarsa lokacin da Taylor ya ke kan karagar mulki, ya yi amfani da dukiyar ƙasa wajen haddasa kisan gilla, facaka da lalata rayuwar wasu ta hanyar azabtarwa. Ya zamanto wajibi a yanzu ya fuskanci hukunci akan waɗannan laifuffuka daya aikata a baya.

A tsakiyar shekara ta 2006 ne dai aka kawar da Charles Taylor daga Freetown zuwa birnin Hague. Shari'ar ta Taylor dai ta samu shaidu da suka hadar da shahararriyar mai kayan kawa Naomi Campell da jigo a fina-finai Mia Farrow. Bayan yanke masa hukunci wanda zai ta'allaka da munin laifin daya aikata dai, Taylor zai yi zaman kaso a kasar Britaniya.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe