1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jagoran tsagerun ynakin Darfur ya gurfana gaban kotun duniya

Mahmud Yaya Azare SB)(AH
April 5, 2022

An gurfanar da Ali Muhammad Ali Abd-Al-Rahman, da aka fi sani da Ali Kushayb tsahon jagoran tsageru a yankin Darfur na Sudan a gaban kotun duniya kan tuhuma 31 na yaki da laifukan cin zarafin dan Adam.

https://p.dw.com/p/49Ufc
Holland, birnin Hague | Shari'ar Ali Kushayb na yankin Darfur na Sudan
Ali KushaybHoto: International Criminal Court/AA/picture alliance

Kotun hukunta manyan laifukan yaki ta ICC da ke birnin Hague a kasar Holland ta soma shari'ar tsohon dan tawayen kasar Sudan Ali Mohammed Ali Abd-Al-Rahman da ta zarga da aikata laifukan yaki da cin zarafin dan Adam a rikicin da aka kwashe shekaru ana tafkawa a lardin Darfur na kasar Sudan.

Ali Mohammed Ali Abd-Al-Rahman mai shekaru 72 da ke zama na hannun daman hambararen shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir, bai amsa laifin da kotun ta tuhume shi ba, daga cikin laifuka 31 da ake zargin tsohon jagoran 'yan tawayen da aikatawa a matsayin shugaban mayakan sa-kai na 'yan Janjaweed da suka yi gwagwarmaya da makamai daga shekarar 2003-2004.

A cewar Karim Khan babban alkalin kotun ta ICC, Ali Abd-Al-Rahman ya taka muhimmiyar rawa wajen jagorancin kisa ga daruruwan mutane gami da cin zarafin mata.

Tun a farkon shekara ta 2020 Ali Kushayb shugaban kungiyar ta 'yan janjaweed ya mika kansa ga kotun ICC.