Kotun ICC ta ce an aikata laifin yaki a rikicin Sudan
January 29, 2024Mai gabatar da kara a Kotun hukunta masu aikata manyan laifuka ta kasa da kasa ICC Karim Khan, ya shaidawa kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya cewa akwai tarin hujjoji da ke nuna cewa masu gwabza fada da juna a yankin Darfur na Sudan sun aikata laifukan yaki.
Karin bayani:Baerbock: Jamus na muradin sasanta rikicin Sudan
A ranar 15 ga watan Afirilun bara ne dai rikici ya barke tsakanin jagoran sojojin Sudan Janar Abdul Fattah al-Burhan da dakarun sa-kai na RSF da ke karkashin Mohamed Hamdan Dagalo.
Yanzu haka dai rikicin ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da dubu goma sha biyu, tare da raba dubbai da muhallansu.
Karin bayani:MDD ta ce an halaka mutane dubu goma sha biyar a yankin Darfur na Sudan
Yanzu haka dai wani rikicin kabilanci tsakanin al'ummar Sudan da kuma Sudan ta Kudu kan ikon wani yanki da ke kan iyakar kasashen biyu, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 54, ciki har da jami'an wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya guda 2, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniyar ta sanar a Litininin din nan.
Hatsaniyar ta fara ne tun da safiyar Asabar din da ta gabata zuwa Lahadi, a yankin Abyei, in ji wani jami'in yankin mai suna Rou Manyiel Rou, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya rawaito.