Kotun kasar Iran ta daure wani dan Amirka
July 16, 2017Wata kotun a kasar Iran ta yanke wa wani dan Amirka hukumcin shekaru goma a kurkuku bayan da ta same shi da laifin kutse ko leken asiri. Ko da shi ke ba ta bayyana sunan sa da kuma lokacin da aka kama shi ba, amma kuma kotun da ke birnin Teheran ta bayyana cikin sanarwrata cewa dan Amirkan ya daukaka kara.
Masu lura da al'amurra dipolomasiyya na ganin cewar wannan shari'ar zata dada haifar da tsamin danganta tsakanin Tehran da kuma Washington. Dama da ita Iran ta daure wasu 'yan kasar ke rike da passport din Amirka a watan Oktoban 2016 da uba da danshi bisa zarghin leken asiri. So da dama Amirka ta nemi da a sake su ba tare da ba ta lokaci ba, amma kuma Iran ta yi watsi da bukatar. Kasashen Iran ta Amirka sun katse huldar dipolomasiyya tsakanin su tun shekarar 1980 wato shekaru 37 da suka gabata.