1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun kolin Amurka ta bai wa Trump damar tsayawa takara

Zainab Mohammed Abubakar
March 4, 2024

Donald Trump na iya tsayawa takarar zaben fidda gwani na 'yan jam'iyyar Republican bayan da kotun kolin Amurka ta yanke hukuncin cewar, cire sunansa ba ya bisa ka'ida.

https://p.dw.com/p/4dA96
Donald Trump
Hoto: Steve Helber/picture alliance/AP

A hukuncin da ta yanke, kotun kolin Amurkar ta yi watsi da hukuncin da kotun kolin jihar Colorado ta yanke a baya, wanda ya ce a cire sunan Trump daga zaben naColorado saboda yana da hannu a cikin rikicin tayar da kayar baya na magoya bayansa ranar 6 ga watan Janairun 2021.

Wannan a cewar kotun jihar a hukuncinta, ya hanashi cancantar yin takara bisa tanadin wani sashi na Kundin Tsarin Mulkin Amurka.

Sai dai kotun kolin Amurkan a daya hannun ta ce Colorado ba ta da hurumin yin hakan, saboda kundin tsarin mulkin Amurka bai bai wa wata jiha damar cire sunan wani dan takarar shugaban kasa daga jerin masu neman kujerar ta tarayya ba.

Hukuncin ya nuna cewa a yanzu babu wata jiha da za ta yi yinkurin soke sunan Trump a zaben na wanta Nuwamba.