Kotun Masar ta daure jagoran adawa Ahmed al-Tantawi
February 7, 2024Wata Kotun kasar Masar ta zartar da hukuncin daurin shekara guda ga 'dan adawar gwamnati Ahmed al-Tantawi, wanda a bara ya so tsayawa takarar shugabancin kasar don fafatawa da shugaba Abdel Fattah al-Sisi.
Karin bayani:Masar ta kama makamai a kayan agaji zuwa Gaza
Wata kungiya mai rajin kare hakkin jama'a ta EIPR ta ce baya ga hukuncin daurin shekara guda a gidan yari, kotun ta ci tarar al-Tantawi Fan din kasar dubu ashirin, daidai da Dalar Amurka 647, tare da haramta masa shiga zabe har na tsawon shekaru 5, bisa samunsa da laifin karya ka'idojin yakin neman zaben shekarar da ta gabata.
karin bayani:Habasha da Masar sun gaza cim ma matsaya kan Kogin Nilu
al-Tantawi dai ya janye shiga zaben watan Disambar bara ne bayan da ya yi zargin muzguna masa da hukumomi suka rinka yi.