1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun Masar ta haramta jam'iyyar FJP

August 9, 2014

Reshen siyasa na kungiyar 'Yan Uwa Musulmi da aka fi sani da FJP ba zai iya tsayar da 'yan takara a zabukan Masar ba saboda kotu ta sokeshi daga fagen siyasa.

https://p.dw.com/p/1CrrY
Hoto: AFP/Getty Images

Wata babbar kotun kasar Masar ta haramta jam'iyyar Freedom and Justice Party da ke wakiltar Kungiyar 'yan Uwa Musulmi a fagen siyasa. Wannan mataki ya zo ne watannin 11 bayan da kotu ta haramta Kungiyar da ta tsayar da Mohammed Morsi takara, ba tare da ambato reshenta na siyasa a wancan lokaci ba.

Hukunci na nufin cewar Jam'iyyar ta 'Yan Uwa Musulmi ba za ta iya tsayar da 'yan takara a zabuka masu zuwa ba. Da ma dai hukumomin mulkin sojen Masar sun riga su ayyanata a matsayin kungiyar da ke gudanar da ayyukan ta'adanci.

Jam'iyar FJP ce ta lashe zaben da aka shirya a Masar bisa tafarkin demoakaradiya bayan juyin-juya halin da ya yi awon-gaba da kujerar mulkin Hosni Mubarak. Sai dai kuma bayan hambarar da Mohammed Morsi da aka zaba karkashin inuwarta, hukumomin kasar sun yi amfani da karfi wajen murkushe boren da suka tayar da nufin yin Allah wadai da yi wa demokaradiya kakar tsaye.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Mohammad Nasiru Awal