1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun Pakistan ta sauke Nawaz Sharif

July 28, 2017

Kotun kolin kasar Pakistan ta sauke faraministan kasar Nawaz Sharif daga mukaminsa na har abada, wani matakin da ake ganin zai kara wa kasar rudanin siyasa.

https://p.dw.com/p/2hJiX
Pakistan Premierminister Nawaz Sharif
Hoto: Reuters/C. Firouz

Kotun kolin kasar Pakistan ta sauke faraministan kasar Nawaz Sharif daga mukaminsa na har abada, wani matakin da ake ganin zai kara wa kasar rudanin siyasa baya ga rigimar tsaro da na arzkin da suka mamaye ta tsawon shekaru. Nawaz Sharif da kotun ta same shi da laifin almundanahana, ya ajiye aiki ne jim kadan da sanarwar yana mai tabbatar rashin ikonsa a gwamnati.

Ya ce koda yake ya rungumi kaddara, yana dai da ja kan yadda kotun ta gudanar da batun, har kuma ta kai ga wannan matakin na sauke shin. Ana sa ran zai bayyana wanda zai gaje shi daga jam'iyyarsa ta masu ra'ayin Islama, a lokacin taron majalisar dokoki da za a yi na zaben sabon jagoran gwamnatin kasar ta Pakistan.