Kotun The Hague ta sake tabbatar da hukuncin ɗaurin shekaru 50 wa Taylor
September 26, 2013Charles Taylor tsohon shugaban ƙasar Liberiya ya sami hukuncin ɗauri a gidan yari na tsawon shekaru 50. Kotun ɗaukaka ƙara ta musamman wa ƙasar Saliyo dake The Hague ta yanke wannan hukuncin yau, bayan da a bara aka sami Mr Taylor da laifuka 11 waɗanda suka haɗa da fyaɗe, da kisar gilla da kuma amfani da ƙananan yara a matsayin sojoji. Wannan hukunci ya zauna ne bayan da Kotun ɗaukaka ƙara ta amince da shi bayan ta gudanar da nata binciken.
Mai sharia George Gelaga King ke nan yake gabatar da hukuncinsa dangane da ƙarar da tsohon shugaba Charles Taylor ya ɗaukaka
Charles Taylor zai ci gaba da kasancewa a hannun kotu na musamman na Saliyo kafin a kammala shirye-shiryen mayar da shi inda zai fuskanci wannan hukunci
A yayin da Charles Taylor zai ci gaba da kasancewa a hannun kotun ya kuma fuskanci hukuncin ɗauri na shekaru 50 mai shigar da ƙara Brenda Hollis na taka tsantsan wajen kwatanta hukuncin a matsayin nasara
"Ba daidai ba ne a ce yau rana ce ta murna ko yin buki, yanayin laifukan da aka tabka ba zasu bari a yi murna ba, amma kuma rana ce ta yin waiwaye kan laifukan da aka tabka da kuma hukuncin da aka yanke, da irin juriyar da waɗanda abin ya shafa suka nuna da ma al'ummomin ƙasar Saliyo"
Matsayin masu shigar da ƙara
Brenda Hollis ta kuma yi wa mutane tunin muhimmancin wannan shari'a da ma hukuncin da aka yanke
Sashen ɗaukaka ƙara yau ya tabbatar da abin da shari'ar farko ya fayyace, cewa shugabanin ƙasashe zasu ɗauki alhakin duk wani laifin yaƙi da sauran laifukan ƙasa da ƙasa da suka tafka, kuma babu wanda ya fi ƙarfin doka, hukuncin yau ya nuna cewa a shugabanci ba ƙarfin iko kaɗɗai mutun zai nuna ba, amma dole ya ɗauki ɗawainiyar duk wasu abubuwan da za su biyo baya
Makomar Charles Taylor
Lauyan Charles Taylor Morris Anyah ya ce wannan shari'a zai yi tasiri kan shari'ar ƙasa da ƙasa, ya yi fatan cewa kotun ɗaukaka ƙarar za ta bi tafarkin hukuncin da aka yanke a kotun hukunta manyan laifukan yaƙi ta Yugoslaviya inda kotun ta wanke wani tsohon jami'in Serbiya daga zarge-zargen da ake yi masa na taimakawa wajen haddasa rigingimu, bayan da ta yanke hukuncin cewa akwai waɗansu mahimman abubuwan da take buƙata kafin ta kai ga yanke irin wannan hukunci
A sakamakon wannan shari'ar dai za a iya cewa an sami sauyi a yanayin yanke hukunci a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa, domin taimakawa wajen haddasa rigingimu na nufin abubuwa daban-daban a kowace kotun da ke The Hague, domin idan da Charles Taylor ya gurfana a gaban kotun da ke hukunta manyan laifukan Yugislaviya ne da wata ƙila an sami sakamako daban, kuma wannan kotun bai fi tazarar kilometa 10 tsakaninta da wannan kotun ba
Duk da cewa lauyan Charles Taylor na takaicin wannan hukuncin ya duƙufa wajen ganin yadda zai tabbatar ya cigaba da ganin 'yan uwa da abokan arziƙinsa.
Martanin 'yan Saliyo dangane da wannan shari'ar
Ga wasu daga cikin ra'ayoyin 'yan Saliyo bayan da aka yanke wannan hukunci
"A tunani na dole ne a sake duba wannan shari'ar, kuma dole mu fahimci abin da ake nufi domin an cika zuwa Afirka a ɗauki shugabaninsu a gurfanar da su ba tare da an gudanar da bincike mai zurfi ba a kuma kira shi adalci"
Wannan kuwa cewa yake yi, ina farin ciki, a gani na an kamanta adalci, kuma wannan zai zama darasai ga sauran shugabanni, domin su san irin matakan da zasu riƙa ɗauka lokacin rikici.
A yanzu haka dai matakin samun kotunan hukunta manyan laifukan yaƙi na ƙasa da ƙasa na fiskantar suka a ƙasashen Afirka, inda shuwagabanin ke ganin kaman su kaɗai ake hukuntawa, kuma yawancinsu na yunƙurin ficcewa daga yarjejeniyar da ta samar da irin waɗannan kotuna.
Mawallafiya: Cintia Taylor/ Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Saleh Umar Saleh