Kotun Togo ta halarta takarar Gnassingbe
March 12, 2015Kotun tsarin mulkin kasar Togo ta amince shugaban mai ci a yanzu Faure Gnassingbe ya sake tsayawa takara a karo na uku a zaben da zai gudana a wata Afirilu mai zuwa, duk kuma da adawa da wani bangare na siyasa ke nunawa. Da ma dai tun bayan da aka kwaswkware kundin tsarin mulkin Togo a shekara ta 2002, doka ta cire shinge da ke kayaade yawan wa'adin da shugaban ya kamata ya yi a kan karagar mulki.
'yan adawa da kuma shugabannin fararen hula sun ta fantsama a kan tituna da nufin taka wa shugaban Gnassingbe birki a kokarin da ya ke yi na yin tazarce. Shi dai Faure wanda ya yi karatu a kasashen Faransa da kuma Amirka ya dare kan kujerar mulki ne a shekara ta 2005 bayan rasuwar mahaifinsa Eyadema wanda ya shafe shekaru 38 a kan kujerar mulki.
Su ma dai daukacin 'yan adawa ciki har da madugunsu Jean Pierre Fabre sun samu amincewar kotun tsarin mulki wajen tsayawa takara a zaben shugaban kasa.