Senegal: Kotun tsarin mulki ta soke kudirin dage zabe
February 16, 2024Kotun tsarin mulkin ta ce kudirin dokar da majalisar dokoki ta amince da shi na dage zaben zuwa watan Disemba ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar da ke Yammacin Afrika.
Babbar kotun da ke birnin Dakar ta kuma soke kudirin dokar da shugaba Makcy Sall ya dauka na yin gyaran fuska ga jaddawalin zaben a daidai lokacin da ya rage makonni uku a gudanar da shi, sai dai amma ta ce saboda jinkirin da aka samu na rashin gudanar da zaben a ranar 25 ga wannan wata na Fabarairu, hukumomi su gaggawa tsayar da sabon jadawalin zaben shugaban kasar.
Karin bayani: 'Yan sandan Senegal sun tarwatsa masu zanga-zanga a Dakar
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Macky Sall ta fara sako fursunonin siyasa domin samar da masalaha ga rikicin siyasar da ya kunno kai a Senegal.