1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An bayar da belin Bobi Wine a Yuganda

November 20, 2020

Rahotannin da ke fitowa daga kasar Yuganda na cewa wata kotu ta bayar da belin magudun adawa Bobi Wine bayan da aka gabatar da shi a gabanta.

https://p.dw.com/p/3lcGk
Robert Kyagulanyi
Hoto: Emmanuel Lubega/DW

Kamun da aka yi magudun adawa Bobi Wine a ranar Laraba ya haifar da zanga-zanaga wace kawo safiyar Jumma'ar nan ta yi sanadiyyar mutuwar mutum 38.


Robert Kyagulanyi wanda ake yi wa lakabi da Bobi Wine ya yi fice a fagen waka a Yuganda kuma daga bisani ya rikide ya koma dan siyasa har ma a yanzu ya zamarwa Shugaba Yoweri Mosevni babban mai adawa a zaben watan Janairu mai zuwa. An kama shi ne bisa laifin karya dokokin corona ta hanyar shirya gangamin yakin neman zaben da ya tara fiye da adadin mutanen da hukumomi suka kayyade.

Sai dai kuma matasa na ci gaba da yin adawa da lamarin ta hanyar zanga-zanga.