Wajibi ne masu mulki su cika wa'adi
May 12, 2019Talla
A watan Disamban da ya gabata ne dai Kramp-Karrenbauer ta karbi ragamar shugabancin jam'iyyarsu ta CDU daga wajen Merkel, sai dai shugabar gwamnatin ta ta ce zata cigaba da jagorantar gwamnatin hadar zuwa karshen wa'adin mulkinsu.
Shugabar jam'iyyar ta nunar da cewar, an zabi Angela Merkel da 'yan majalisar Jamus din ne na tsawon wa'adin mulki, kuma al'umma na kyautata zaton zasu tafiyar da ayyukansu da ke tattare da zaben har zuwa karshe.
A 'yan wannin nan kafofin yada labaru na Jamus sun yi ta yada jite-jite dangane da yiwuwar Merkel ta yi murabus daga mukaminta na jagorantar gwamnatin hadakar, kafin karshen wa'adin mulkinta a 2021.