1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kudirin Hitler a kan nahiyar Afirka

Umaru AliyuSeptember 1, 2014

Jamus ba ta ji dadin yadda kasashen Birtaniya da Faransa suka yi rabon gado da kasashen Afirkan da ta yiwa mulkin mallaka gabanin yakin duniya na biyu ba.

https://p.dw.com/p/1D4nS
Adolf Hitler 1939
Hoto: Getty Images

Lokacin da Adolf Hitler ya kama mulki a watan Janairu na shekara ta 1933 Jamus bata da kasashe a ketare da take wa mulkin mallaka. A bayan nasarorin da suka samu lokacin yakin duniya na daya kasashen Ingila da Faransa sun raba kasashen da Jamus ta yi wa mulkin mallaka a tsakaninsu. Daga cikin kasashen kuwa harda Kamaru da Togo da Tanzaniya da Ruwanda da kuma Burundi. Sun kuma mika yankin kudu maso yammacin Afirka wato Namibiya a yau karkashin mulkin mallakar Afirka ta kudu.

Magoya bayan Hitler a wancan lokaci sun yi matukar bakin cikin asarar wadanan yankuna na Afirka da Jamus ta yi, ko da yake Hitler shi kansa ya fi maida hankalinsa ne ga nahiyar Turai inda yafi dora muhimmanci ga yunkurin fadada daular Jamus ta hade da Faransa da Tarayyar Soviet. Nahiyar Afirka bata cikin jerin yankunan da Hitler din yake da burin fadada daularsa zuwa can inji masanin tarihin Jamus, Andreas Eckret na cibiyar nazarin al'amuran Asiya da Afirka a jami'ar Humboldt ta Berlin.

"Afirka bata cikin yankunan da ya rika hangensu a burinsa na mamaye duniya baki daya. Ga Hitler wasu yankunan duniya sun fi zama masu muhimmanci. To amma duk da haka bai nuna adawa da sha'awar da wasu makusantansa suke nunawa game da nahiyar ta Afirka ba."

Parade in Brest-Litowsk Polen 1939
Sojojin Jamus na yin Fareti yayin yakin duniya na biyuHoto: picture-alliance/akg-images

Burin Jamus ta mallaki Afirka

Daga cikin wadannan makusanta na Hitler kuwa har da 'yan siyasa masu fada aji wadanda suka dauki yarjejeniyar Varssails da ta kawo karshen yakin duniya na daya a matsayin kaskantarwa ga Jamus. A shekara ta 1934 irin wadannan 'yan siyasa suka kirkiro wani ofishi na musamman da zai kula da batun samarwa Jamus kasashen da zata yiwa mulkin mallaka a ketare. Bayan shekaru biyu, shi kansa Hitler ya nemi a sake mayarwa Jamus yankunan da ta yi asararsu a ketare. Masanin tarihi na kasar Kamaru Parima Kum'a Ndumbe III marubucin wani littafi mai suna "Me Hitler ya zo nema Afirka?" ya ce shugaban gwamnatin daular ta Jamus ya yi fama da matsin lamba ne daga fannin tatalin arzikin kasar ciki har da masu baiwa Hitler taimakon kudi kamar babban bankin Jamus da bankin Deutsche Bank da kuma wani kamfani mai suna IG Farben.

Bugu da kari kuma akwai Jamusawa masu yawa da ke zaune a yankunan na Afirka a lokacin da Jamus ta yi asarar mulkin mallakarta a kansu a karshen yakin duniya na daya. Kungiyoyin Jamusawa a kasashen Kamaru da Tanzaniya da Namibiya sun ci gaba da rayuwarsu a can ne kamar dai suna zaune a Jamus inji Andreas Eckert.

"A duk wadannan yankuna an kak-kafa rassan jam'iyar Hitler ta NSDAP. A lokacin da aka fara yakin duniya na biyu aiyukansu sun zama masu wahala saboda Jamusawa da yawa an kama su an kuma kaisu sansanonin tsare firsinonin yaki. Amma duk da haka a wadannan yankuna na mulkin mallakar Jamus an sami wadanda suka lashi takobin ganin tilas sai yankunan sun ci gaba da zama karkashin daular Jamus".

Kokarin Jamus na kafa daula a nahiyar Afirka

A karshen shekaru na 30 da kuma farkon fara yakin duniya na biyu shirye-shirye sun yi nisa game da samarwa Jamus sababbin yankuna a Afirka da zasu zama karkashin mulkin mallakarta. Jamus ta sami nasarori a shekarun farko na yakin abin da ya sanya 'yan Nazi suka ci gaba da wuce gona da iri a burinsu na neman mallakar duniya baki daya. Nasarorin da 'yan Nazin suka samu kan Faransa da Beljiyam sun sanya sun kai ga kudirin cewar kame kasashen Afirka abu ne mai sauki. Ofishin kula da batun mulkin mallaka na Jamus da farko ya bayyana burin kirkiro wata daular mulkin mallaka a yankin mashigin Gini tun daga Ghana ta yanzu har zuwa Kamaru. Shugaban ma'aikatar Kurt Weigelt wanda kuma shine shugaban bankin Deutsche Bank ya yi imanin cewar wannan yanki mai arzikin albarkatun kasa zai dace da cimma dukkanin bukatun daular Jamus.

Britischer Soldatenfriedhof in Tobruk in Lybien
Kaburburan sojojin kasashen Turai da na Afirka da suka mutu a yakin duniya na biyuHoto: picture-alliance/dpa

Daga baya mahukuntan na Jamus sun ce burinsu shine su mamaye karin yankuna na Afrika har zuwa tekun Indiya amma ba tareda sun taba Afirka ta Kudu ba saboda daular ta Jamus ta dauki masu mulkin waariya a Afirka ta kudu a matsayin abokan hadin gwiwa ne na neman malakar nahiyar Afirka baki daya, kasancewar burin Jamus hine ta bi tafarkin wariya da nuna banbancin launin fata kamar dai a Afirka ta kudun. Wannan buri na Hitler bai cika ba saboda sojojinsa da na Italiya sun sha kaye a hannun Ingila. Lokcin da Hitler ya fara shan kaye a fagen daga na gabas daga hannun daular Soviet mafarkinsa na mallakar nahiyar Afirka ya rushe gaba daya.

Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Lateefa Mustapha Ja'afar/ USU