Kujeru ƙalilan shugaban Iran ya lashe
March 3, 2012Shugaba Mahmud Ahmadinejad na Iran na fiskantar koma baya a zaɓen 'yan majalisa ya gudana ranar lahadi. Alƙaluman farko sun nunar da cewa kujerun da ɓangaren gwamnati ya lashe bai taka kara ya karya ba daga cikin 290 da majalisar ta ƙusa. Maimakon haka ma, masu ra'ayin riƙau ƙarƙashin shugaban majalisa Ali Larjani ne suke kan gaba da yawan ƙuri'u da kuma kujeru a halin yanzu. Gobe lahadi idan Allah ya kaimu za a bayar da cikakken sakamakon zaɓen ƙasar ta Iran.
Hukumomin Teheran sun nunar da cewa kashi 60% na waɗanda suka yi rejista ne suka kaɗa ƙuri'unsu. Sai dai rabin adadin waɗanda suka cancata ne suka fito a babban birnin ƙasar ta Iran. 'Yan adawa da tun a baya suka yi kira da a ƙaurace ma zaɓen, sun danganta shi da na jeka na yi ka . Wasu daga cikin shugabannin na adawa ciki kuwa har da Mehdi Karoubi suna fiskantar ɗaurin talala.
Wannan zaɓen 'yan majalisa da ke zama na farko tun bayan sabotan wa'adin mulkin Ahmadinejad a shekara ta 2009, ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da takaddama da Iran game da shirinta na nukiliya.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Saleh Umar Saleh