Makamin roka na H3 ya tarwatse aJapan
March 7, 2023Talla
Kamfanin dillancin labarai na Japan Iqna ya rawaito cewar makamin roka samfurin H3 da aka harba daga Tanegashima da ke a kudu maso yammacin kasar da ke tafe da kumbon ya gaza. Hukumar sararin samaniya ta Japan Jaxa ta ba da ummarnin tarwatsar da shi, jim kadan bayan tashinsa sakamakon gazawar da har yanzu ba a san dalili ba.
Wannan gazawa ita ce ta biyu a jere ga wannan sabuwar na'urar ta harba kumbo a sararin samaniya, wanda Japan ta sanya fata mai yawa na kasuwanci da sauran harkoki tattalin arziki a kanta. wadda aka kwashe shekaru 30 ana kerawa. A tsakiyar watan Fabrairu ne rokar ta gaza tashi, sakamakon wata matsala da aka samu da na'urori masu kara kuzari, lamarin da ya tilasta wa hukumar Jaxa ɗage tashin jirgin na farko.