Bukatar mutunta 'yancin tsohon sarkin Kano
March 11, 2020Amnesty International din dai ta ce takaita 'yanci na walwala da kuma hana shi damar ganawa sun saba kundin tsarin mulkin kasar da ya tabbatar da jerin 'yancin kan kowa.
Kuma a fadar kungiyar ya zama wajibi ga mahukunta na kasar da su kare tare da mutunta daukacin yancin sarkin dake garin Awe a halin yanzu.
Takkadama ta yi nisa a cikin tarrayar Najeriyar game da hallascin tsare sarkin da lauyoyinsa ke fadin suna hanyar kotu da nufin kalubalantar cigaba da tsare shi dama kai shi zuwa garin Awe maimakon birnin Legas da ya zabi kasancewa.
To sai dai kuma har ya zuwa yanzu an gaza gano masu ruwa da tsaki da kokarin tsare sarkin a Awe bayan da jihar Kanon ta ce bata da hannu a kokari na kai shi kanon.
To sai dai kuma an wata ganawar sirri a tsakanin shugaban kasar da gwamnan jihar Nasarawa dake masaukin sarkin da safiyar yau din nan.
Duk da cewar kau da sarkin daga mulki tare da sauya masa garin zama yana zaman al'ada a cikin tarrayar Najeriya, kotunan kasar sun yanke jerin hukuncin da ke fadin tsarin ya sabawa kundin tsarin mulki na kasar kuma yana zama na haramun.
Akwai dai yiwuwar fadawa a cikin jani in jakar shari'a a tsakanin magoya bayan sarkin da ke fafutukar tabbatar da 'yancin nasa ko ana ruwan kibau, da kuma hukumomin da suke yi wa 'yancin na Sanusi kallon barazana mai girma ta siyasa a cikin tarrayar Najeriyar da hadari na siyasar ya fara nuna alamun kankama.