Kungiyar Amnesty ta zargi hukumomin kasar Turkiya
April 1, 2016Kungiyar ta zargi hukumomin na turkiya ne da laifin maida 'yan gudun hijira da karfi da yaji ya zuwa kasar Siriya bayan da suka guje wa yake-yaken kasar ta Siriya. Cikin wata sanarwa ce dai da ta fitar a wannan Jumma'a kungiyar ta mai fafutukar kare hakin dan Adam ta ce ta samu labari ne daga shaidu da abubuwan suka faru a kansu kamar yadda Jean-François Dubost, shugaban sashen kula da kariyar al'umma a kungiyar ta Amnesty reshen kasar Faransa ya yi tsokaci:
"Mun je kasar Turkiya ba da dadewa ba, kuma mun je yankunan iyakokin kasar da Siriya, sannan mun tattara bayannai daga iyalai da dama da suka tabbatar an mayar da su zuwa kasar ta Siriya bayan da suka iso Turkiya kuma bayan da jami'an tsaro suka bincike su."
Hakan dai na zuwa ne kwanaki kalilan kafin sake mayar da gungun farko na 'yan gudun hijira da aka kora daga Turai zuwa kasar ta Turkiya kamar yadda yarjejeniyar da aka amince da ta ranar 20 ga watan jiya na Maris.