Kungiyar AU ta dakatar da Burkina Faso
January 31, 2022Talla
A sakon da kungiyar ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce ta dakatar da kasar daga kungiyar har sai an mayar da ita tafarkin dimokaradiyya. Shugaban Majalisar gudanarwar kungiyar Moussa Faki Mahamat tuni ya yi tir da juyin mulkin.
Ita ma Kungiyar Yammacin nahiyar Afirka ECOWAS ta dakatar da Burkina Faso daga kungiyar a ranar Juma'ar da ta gabata tare da turawa da tawaga don ganawa da majalisar mulkin soji a kasar a karshen mako.
Kasar Burkina Faso dai ta sha fama da matsalolin tsaro tun bayan samun 'yancin kanta daga Faransa a shekarar 1960.