Kungiyar ETA ta fara sabuwar gwagwarmaya da gwamnatin Spain
August 26, 2007Talla
Kungiyar ´yan awaren yankin Basque na kasar Spain wato ETA ta ce ta shiga wata sabuwar gwagwarmayar daukar makami don matsawa gwamnatin Spain lamba. Jaridar masu ra´ayin mazan jiya ta ABC Espana ta rawaito a yau lahadi cewa wannan sabuwar gwagwarmayar na nufin kungiyar ETA ba zata yi sako sako ba wajen kai hari don ta yi kisa. A ranar juma´a da ta gabata kungiyar ta ETA ta kawo karshen shirin tsagaita wuta da ta ayyana cikin watan yuni inda ta kai wani harin bam akan barikokin ´yan sanda a garin Durango dake arewacin yankin na Basque. Mutane biyu suka samu raunuka a wannnan hari. Jaridar ta ce manufar sabon shirin kai hare haren dai shi ne a matsawa gwamnatin ´yan socialist ta Spian ta shiga tattaunawa da kungiyar mai daukar makami. To sai dai FM Jose Luis Rodriguez Zapatero yayi watsi da kowane shiri na tattaunawa da kungiyar yana mai cewa dole sai ta daina ta da zaune tsaye.