Kungiyar EU na kara shiri kan tsaro
January 20, 2015Kungiyar Tarayyar Turai na kara daukar matakan hadin kai na tsaurara tsaro da kasar Turkiya da ma wasu kasashen Larabawa.
Bayan kammala taro da mambobin kungiyar kasashen Larabawa a jiya Litinin shugabar shirin harkokin kasashen waje daga kungiyar ta EU Federica Mogherini, ta bayyana cewa kungiyar ta EU ta shirya tura wasu jami'an tsaro da zasu yi aiki na tallafawa shirin karya lagon shirye-shiryen ta'addanci.
Ta ce domin tabbatar da ganin dorewar dangantakar tsakanin su da kasashen na Larabawa zasu kafa wani shiri mai tsari da za a rika bibiya. Nan gaba kadan ne kuma cikin makonni zasu kaddamar da wasu aikace-aikacen a wasu kasashe da suka hadar da Turkiya da Masar daYemen da Aljeriya da kasashen yankin Gulf.
Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Umaru Aliyu