Kungiyar EU na sake tuhumar Facebook
April 6, 2018Kamfanin Facebook ya dauki alhaki na cewa ya yi wasarairai da bayanan kimanin mutane miliyan biyu da dubu dari bakwai daga Kungiyar Tarayyar Turai kamar yadda kungiyar ta bayyana a wannan rana ta Juma'a, inda ta ce za ta ci gaba da neman karin amsar wasu tambayoyi daga baban kamfanin na sada zumunta.
A makon da ya gabata ne kungiyar ta EU ta nemi kamfanin Facebook ya bata bayani kan yawan adadi na mutanenta da aka yi musayar bayanansu da kamfanin nan mai alaka da harkokin siyasa wato Cambridge Analytica. Facebook ya tabbatar da cewa mutane miliyan biyu da dubu dari bakwai ne daga EU abin ya shafa a cewar Christian Wigand da ke magana kan harkokin da suka shafi dokoki a EU.
A ranar Alhamis shugaban kamfanin na Facebook Mark Zuckerberg ya bayyana cewa mutane miliyan 87 ne a fadin duniya suka fada rikici na gaza kare bayanan sirrin jama'a da kamfanin ya yi, lamarin da ya jefa tunanin al'ummar duniya cikin rudani dangane da kare masu bayanai a shafukan na ci gaban fasaha.