1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar EU na son a koma tebur kan Siriya

Yusuf Bala Nayaya
April 16, 2018

Bayan da Amirka da kawayenta suka kaddamar da hare-hare, ministocin harkokin waje daga Kungiyar Tarayyar Turai a taronsu na birnin Luxembourg a wannan Litinin sun bayya tattaunawar zaman lafiya da zama fifiko.

https://p.dw.com/p/2w882
Luxemburg EU-Außenministertreffen
Taron ministocin waje na Kungiyar EU a Luxemburg Hoto: Reuters/E. Dunand

Amirka da Birtaniya da Faransa sun kaddamar da hari kan rumbun ajiyar makamai mallakar kasar ta Siriya a ranar Asabar a matsayin ramuwar gayya bayan zargin mahukuntan na Damascus da kaddamar da hari ta hanyar amfani da makami mai guba a Douma ranar bakwai ga watan Afrilu, harin da Siriya da Rasha suka ki aminta da hannunsu a ciki.

A cewar ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas da isar sa wajen taron na  Luxembourg ya ce dole kowa ya shiga wannan tattaunawa kafin akai ga warware rikicin. Ita kuwa shugabar sashin kula da harkokin waje a EU Federica Mogherini ta ce nan gaba a wannan wata Tarayyar Turai da MDD za su jagoranci wani zama kan lalubar mafitar a rikicin na Siriya.