SiyasaAsiya
EU da China sun tattauna kan cin zarafi
September 15, 2020Talla
Jami'an kungiyar tarayyar Turai ta EU sun yi kira ga China da ta bude kofofin kasuwanci ta kuma gyara mu'amullarta da 'yan fafutuka. Wannan na zaman wani bangare na abubuwan da bangarori biyun suka tattauna a wurin taron bunkasa kasuwanci a tsakaninsu da ya gudana a ranar Litinin.
A taron wanda na bidiyo ne shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi murnar cewa a karshen taron sun tattauna abubuwa masu tsauri wadanda da farko ba su fahimci juna a kai ba musamman kan batun gallaza wa kananan kabilu da 'yan fafutuka da China ke yi.
Sai dai duk da dogon Turancin da EU da China suka fafata, a karshe sun amince su rinka cinikayyar kayan abinci a tsakaninsu.